Manyan Labarai Guda 9 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Alhamis
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 9 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis 3 ga watan Disamba. Ku duba domin ku same su.
1. Dasuki Ya Bayyana Odili, Bode George A Matsayin Wadanda Ya Bawa Kudi
Kanar Sambo Dasuki mai murabus ya bayyana cewa da Dacta Peter Odili da Cif Bode George suna cikin wadanda ya bawa kudaden makami daya sata.
2. Bafarawa Ya Musanta Cewa Ya Amshi Kudi Daga Wajen Dasuki
Tsohon gwamnan JIhar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya musanta cewa ya amshi kudi saga hannun Sambo Dasuki.
3. Wani Soja Ya Halbe Wata Mai Zanga Zangar Biafra
Kungiyar MASSOB ta sha alwashin cigaba da zanga zanga bayan da wani sojan ruwa ya halbe wata mai yin zanga zanga jiya a garin Onitsha.
4. Zaben Bayelsa: Yan Takara 6 Sun Janye Sun Bar Ma Sylva
Kasa da awa 48 a fara zaben jihar Bayelsa, yan takara daga jam’iyyu guda 6 sun janye sun bar ma Timipre Sylva na APC. Sun bayyana cewa sunyi haka ne saboda kaunar da suke yi ma jihar.
5. Wani Lauya Ya Kai Buhari, AGF Kara A Kotu
Wani lauya mai Suna John Nwobodo ya kai Shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban mai gurfanar da Shari’a na Najeriya kara kotu saboda wariyar aiki da Shugaba Buhari yayi ma ministocin shi.
6. Zaben Bayelsa: An Halbe Wani Jigon APC A Jihar
Yan bindiga sun halbe wani jigon APC mai suna Diseyw Dickson, wanda shine mataimakin ciyaman na mazabar Odi Kolo Kuma-Oppkuma. Wadanda sukayi halin suna sanya be da kayan sojoji.
7. Shugaba Buhari Ya Karbi Ziyarar Bukola Saraki A Villa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ziyarar shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki a fadar shugaban kasa a jiya.
8. Wata Mata Ta Tona Ma Kanta Asiri Akan Lalatattun Da Takeyi
Mata matar aure mai suna Nnenna, a jihar Legas, ta tona ma kamata asiri cewa tana yin lalata da maza ne saboda mijinta baya biya mata bukata sosai.
9. Wata Yar Wasan Nollywood Ta Sha Duka Saboda Wata Mata Ta Kama Ta Da Mijin Ta
Yar wasan kwaikwaiyo ta Nollywood ta sha duka bayan da wata mata ta kama ta da mijin ta a wani wasan mai suna Hustlers. Film din dai yana nuna rayuwar aure da yadda wasu ke neman duniya ido rufe.
The post Manyan Labarai Guda 9 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Alhamis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.