EFCC Ta Gurfanar Da Dokpesi A Gaban Kotu
Hukumar hana almundahana ta gurfanar da Shugaban Daar Communications, Cif Raymond Dokpesi a Laraba 9 ga watan Disamba a kotun Abuja.
Dokpesi wanda wani jigo ne na jam’iyyar PDP an gurfanar dashi saboda zargin satar kudi da wasu laifuka.
Amma Dokpesi ya bayyana cewa baida laifi akan zargin da hukumar ke yi ma shi. Mai Shari’ah Gabriel Kolawole ya bada umurni a cigaba da tsare Dokpesi a hannun EFCC har sai an saurari ko za’a iya bada belin shi a yau 10 ga watan Disamba ko a’a.
Lokacin sauraron koken, Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs (SAN) ya bayyana cewa Suna zargin Dokpesi da amsar kudaden da suka Kai Naira Biliyan 2.1 daga ofishin NSA a lokacin Dasuki.
Mai gurfanarwar ya bayyana cewa hakan ya saba ma dokar yadda ma’aikatan gwamnati ya kamata su gudanar da kansu.
Bayan da ya gama sauraron su, Mai shari’a Kolawole Sai ya daga shari’ar zuwa watan Febrairu 17, 18, da kuma 2,3 ga watan Maris.
Kimanin Mako 2 ke nan daya wuce EFCC Ta kama Dasuki, Dokpesi, Bafarawa da kuma Yuguda akan zargin satar kudin gwamnati.
The post EFCC Ta Gurfanar Da Dokpesi A Gaban Kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.