Hukumar DSS Ta Sake Kama Dasuki
Hukumar DSS ta sake kama tsohon mai ba shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.
Kanar Sambo Dasuki
Wannan na zuwa ne bayan da kotu ta bada umurni a saki Kanar Sambo Dasuki dake gidan yari dake Kuje, Abuja, bayan da ya cika sharuddan bada Beli.
Hukumar DSS dai ta kama Dasuki tare da Bafarawa, Yuguda da kuma wani babban Jami’in hukumar Kamfanin mai na Najeriya NNPC.
Lauyan Dasuki Ahmed Raji (SAN) ya tabbatar ma da Daily Trust cewa an sake kama Dasuki. Haka zalika shima Cif Obafemi Femi Fani Kayode ya bayyana cewa DSS ta sake kama Dasuki a indabya bayyana haka a shafin Twitter din shi.
The post Hukumar DSS Ta Sake Kama Dasuki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.