Babu abinda zanyi illa na share hawaye, Buhari mun gode inji- Ezekwesili
Shugaban rajin ganin an dawo da ‘yan matan chibok kuma tsohuwar ministan ilimi wato Oby Ezekwesili, ta nuna farin cikin ta game da sako ‘yan matan Chibok guda 21 da akayi garkuwa dasu.
An dai bayyana cewar, da safiyar ranar Alhamis din nan ne 13 ga watan Oktoba, wa’annan kungiyar masu hatsarin gaske wato ‘yan Boko Haram, suka saki ‘yan matan Chibok guda 21 cikin su 200 da suka sace.
Acewar mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, an saki ‘yan matan su 21 wanda a yanzu suna ofishin hukumar bincike na farin kaya wato (DSS).
Haka kuma, fadar shugaban kasar dai tace, andai saki ‘yan matan ne tare da hadin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta duniya tare da gwamnatin Swiss da kuma gwamnatin tarayya.
Shugan masu rajin ganin an ceto da ‘yan matan chibok din dai tayi amfani da shafinta na Tweeter wajen godema shugaban kasa Muhammadu Buhari, a inda ta nuna murnan ta matuka dangane da sakin ‘yan matan Chibok din.
The post Babu abinda zanyi illa na share hawaye, Buhari mun gode inji- Ezekwesili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
