Добавить новость
ru24.net
Все новости
Октябрь
2016

Bamu shiga filin daga ba: Avengers sun yi Allah wadai da shugaba Buhari

0

Daga Edita: Bayan an dauki kusan wata guda ba’a ji duriyarsu ba, Neja Delta Avengers (NDA) ta rubuta wata wasikar bayyane zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari. Gungun na Kira ga shugaban da ya daina yi masu batanci. Sun ce hannayen shugaban na ‘jike da jinin Ken Saro Wiwa” wani marubuci kuma dan rajin ‘yancin bil-adama.

Majalisar koli ta NEJA DELTA AVENGERS tace ya zama dole ta rubuta ma shugaba Muhammadu Buhari wasika domin ci gaban da yayi yana yi masu batanci tun lokacin da mayakanmu suka tsagaita wuta daga fadan cetar da Neja Delta daga mulkin mallaka na tattalin arziki wanda Najeriya ke yi ma yankin.

KU KARANTA: Najeriya tayi asaran N90 billion sanadiyar hare-hare a Neja Delta

Muna mamakin kalamai irin su “manufar tsagerun Neja Delta shine su yima Najeriya mulkin mallaka na tattalin arziki”. “Wadanda suka sace arzikin kasa ke bayan tsagerun Neja Delga”….A wajen paretin yaye daliban makarantar horon sojoji (NDA) kashi na 63, inda kayi maganganu na yaudara da kuma barazanar daukar matakan soji in ya zama dole domin tunkarar rikicin yankin Neja Delta tun da ka bude hanyar tattaunawa ta hannun jami’an tsaron kasa da kuma kampanonin kasa da kasa

The post Bamu shiga filin daga ba: Avengers sun yi Allah wadai da shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса